Hebrews 3

Yesu Ya Fi Musa

1Saboda haka, ʼyanʼuwa tsarkaka, waɗanda suke da rabo a kiran nan na sama, ku kafa tunaninku a kan Yesu, manzo da kuma babban firist wanda muke shaidawa. 2Ya yi aminci ga wanda ya naɗa shi, kamar yadda Musa ya yi aminci ga dukan gidan Allah. 3An ga Yesu ya cancanci girma fiye da Musa, kamar yadda mai ginin gida ya fi gidan daraja. 4Gama kowane gida yana da wanda ya gina shi, amma maginin dukan abu Allah ne. 5Musa ya yi aminci a matsayin bawa cikin dukan gidan Allah, yana ba da shaida a kan abubuwan da za a faɗa nan gaba. 6Amma Kiristi mai aminci ne kamar ɗa a gidan Allah. Mu kuwa gidansa ne, in muka tsaya gabanmu gaɗi da kuma begen da muke taƙama a kai.

Gargaɗi A kan Rashin Bangaskiya

7Kamar dai yadda Ruhu Mai Tsarki ya ce:

“Yau, in kuka ji muryarsa,
8kada ku taurare zukatanku,
yadda kuka yi a tawayen nan,
a lokacin gwaji a hamada,
9inda kakanninku suka gwada ni, suka kuma jarraba ni
ko da yake a cikin shekaru arbaʼin sun ga abin da na yi.
10Shi ya sa na yi fushi da wancan zamani,
na kuma ce, ‘Kullum zukatansu a karkace suke,
ba su kuma san hanyoyina ba.’
11Saboda haka na yi rantsuwa a cikin fushina,
‘Ba za su taɓa shiga hutuna ba.’ ”
Zab 95.7-11

12Ku lura fa, ʼyanʼuwa, cewa kada waninku yǎ kasance da zuciya mai zunubi marar bangaskiya da takan juye daga bin Allah mai rai. 13Sai dai ku ƙarfafa juna kullum, muddin akwai lokacin da ana ce da shi Yau, don kada waninku yǎ zama mai taurin zuciya ta wurin ruɗun zunubi. 14Mu masu tarayya ne da Kiristi idan mun riƙe bangaskiyarmu da ƙarfi daga farko har zuwa ƙarshe. 15Kamar yadda aka faɗa cewa:

“Yau, in kuka ji muryarsa,
kada ku taurare zukatanku
kamar yadda kuka yi a tawayen nan.”
Zab 95.7, 8

16Su wane ne suka ji suka kuma yi tawaye? Ba su ne duk waɗanda Musa ya bi da su daga Masar ba? 17Da su wane ne kuwa ya yi fushi har shekaru arbaʼin? Ba da waɗanda suka yi zunubi, waɗanda suka mutu a hamada ba? 18Kuma ga su wane ne Allah ya rantse cewa ba za su taɓa shiga hutunsa ba, in ba ga marasa biyayyan nan ba? 19Saboda haka mun ga cewa ba su iya shiga ba, saboda rashin bangaskiyarsu ne.

Copyright information for HauSRK